fidelitybank

Ba na fargabar kamu kuma ba zan gudu ba – El-Rufa’i

Date:

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El- Rufai ya ce ba zai yi gudun hijira ba duk da raɗe-raɗin da ake yi na cewa ana shirin kama shi tare da azabtar da shi.

El Rufai ya faɗi haka ne a martanin da ya mayar a shafinsa na X bayan wani mai amfani da shafin ya wallafa cewa ya samu bayanai masu ƙarfi da ke nuna ana shirin kama El Rufai.

”Na daɗe ina jin waɗannan raɗe-raɗin kan kama ni da tsare ni da kuma azabtar da ni a wani ɗakin azabtarwa da ke ofisihin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ( wurin da ake zargin an azabtar ta Emefiele domin ya bar aiki a matsayin gwamnan CBN), tun watan Yulin 2024 lokacin da aka fara yaɗa rahoton majalisar dokokin jihar Kaduna” in ji shi.

Ya kuma ce an aika irin waɗannan sakonnin barazanar ta hanyar abokai da ƴan uwanshi da dama saboda ana so ya yi ji tsoro ya yi gudun hijra da kanshi, sai da El Rufai ya ce ” ba zan yi hakan ba”.

Ya ce kafin ranar 20 ga watan Fabrairu zai dawo Najeriya, ya kuma ce ya dakatar da karatun da yake yi da kuma shirin koyon wasu harsuna zai dawo gida Najeriya, domin a cewarsa ba zai ci gaba da yin shiru ba.

El Rufai ya kuma ce kamawa da tsarewa da kuma azabtar da abokan hamayya a siyasa ba sabon abu ba ne, ”ni kaina an kama ni kuma an kulle ne sau uku a baya saboda bayyana ra’ayi na kan gwamnatocin baya.” a cewarsa.

A ƴan kwanakinnan dai ana ta samun ce-ce-ku-ce tsakanin tsohon gwamnan Kaduna El Rufai da ƴaƴan jam’iyya mai mulki na APC da kuma rashin jituwa da ake zargin akwai tsakaninsa da gwamnan jihar na yanzu Uba Sani.

network news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp