Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a ranar Juma’a, ya nesanta kansa da wadanda ake zargin shugaban kasa Muhammadu Buhari da wawure kudaden kananan hukumomi.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasar ya dora laifin rashin ci gaban al’umma a yankunan su, inda ya nanata cewa gwamnonin jihohi na yin ta’ammali da kudaden da ake bai wa kananan hukumomin Najeriya duk wata.
Da yake mayar da martani kan wannan zargi a Asaba ta bakin babban sakataren yada labaransa, Olisa Ifeajika, gwamna Okowa wanda kuma shine mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa abin takaici ne ga shugaba Buhari ya furta irin wannan “kalamai. ”
“Ina so in ce Shugaba Buhari a matsayinsa na wanda ke da cikakken bayani kan al’amuran da ke faruwa a kasar nan, ya san gwamnonin da suka fada cikin wannan fanni na wadanda ake kira ‘barayi’ da yake magana a kai.
“Dr Ifeanyi Okowa ba ya wurin. Ya kasance daya daga cikin gwamnonin farko da suka rungumi cin gashin kan kananan hukumomi lokacin da aka amince da shi, kamar yadda shugaban kasa ya yi da bangaren shari’a da na majalisa,” inji shi.