Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ,ba ya burin zama shugaban kasa a 2023.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels TV’s Politics A Yau Litinin.
Ya ce shi da masu tunani suna cikin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) don sauya halin da ake ciki da kuma ceto Najeriya daga durkushewa baki daya.
Kwankwaso ya ce, “Mun gaji da tsohon tsarin kamar yadda yake a yau. Shi ya sa muke cikin NNPP don kawo canji. Hanya da yadda abubuwa ke faruwa a kasar nan ba su da kyau. Kowa ya damu da tsaro, tattalin arziki ba shine mafi kyau ba. Duk sauran bangarorin ilimi da al’adu; komai a dunkule yake. In ji Daily Trust