fidelitybank

Ba mutumin da ya kamu da cutar Anthrax a Najeriya – NCDC

Date:

Hukumar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa ta NCDC ta ce, har yanzu cutar Anthrax da wasu dabbobin ke fama da ita ba ta yaɗu zuwa ga bil-adama ba.

gidan Talbijin na ƙasa NTA, ya ambato shugaban hukumar, Dakta Nasir Ahmed na cewa, hukumar na ci gaba da lura tare da sanya idanu, musamman a garin Suleja inda cutar ta fara ɓulla.

Gwamnatin ƙarƙashin ma’aikatar lafiya na ƙarfafa gangamin wayar da kai kan alamomin cutar da yadda za a kauce wa ɗaukar ta, musamman a masarautar Suleja da ke jihar Naija.

Sarkin Suleja Muhammadu Auwal Ibrahim ya yi kira da hakiman masarautar da su kai rahoton rashin lafiyar dabbobi a yankunansu, tare da kauce wa cin naman da likitocin dabbobi ba su tantace lafiyarsa ba.

Tuni dai gwamnatin ƙasar ta bayyana sayen alluran riga-kafin cutar domin yi wa dabbobi a garin Suleja, inda cutar ta fara ɓulla.

Dabbobi na gida da na daji na kamuwa da cutar ne idan suka shaƙe ta daga ƙasa wadda ke ƙunshe da ƙwayoyin cutar ko kuma suka ci ciyawa ko shan ruwan da ke ɗauke da ita.

Dabbobin da suka fi kamuwa da cutar sun haɗa da shanu da tumaki da awaki da kuma barewa.

Haka kuma likitoci sun ce mutane na kamuwa da cutar a lokacin da suka yi cuɗanya da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka taɓa wani abu da ya fito daga jikin dabbobin.

A baya-bayan nan dai hukumomin Najeriya sun bayyana ɓuallar cutar a jihar ta Naija, lamarin da ya sa hukumomin lafiyar ƙasar yin gargaɗi game da cin naman dabbobin da ba su da lafiya

vanguardnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp