fidelitybank

Ba mune muka jefa Najeriya cikin talauci ba – Gwamnoni

Date:

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun ce, sun yi mamakin yadda ƙaramin Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare na ƙasa, Clem Agba ya zarge su da jefa Najeriya cikin talauci.

A watan Nuwamba ne Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce mutum miliyan 130 ne a ƙasar ke fama da talauci, kusan kashi 63 cikin 100 na a’umar ƙasar.

To sai dai a wata sanarwa da ƙungiyar gwamnonin ƙasar suka fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran ƙungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo, ta bayyana kalaman ministan da cewa abu ne da bai kamata ba, kuma babu kanshin gaskiya a cikin kalaman ministan.

Gwamnonin sun ce iƙirarin  da ministan ya yi cewa gwamnonin sun yi watsi da al’ummar karkara – ba shi da tushe balle makama.

A cikin makon da ya gabata ne dai ƙaramin ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare Clem Agba a wani taro da ya yi da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ya ɗora alhakin katutun talaucin da ke damun ƙasar kan gwamnonin jihohi

legit.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...
X whatsapp