fidelitybank

Ba mu yarda Tinubu ya afkawa Nijar ba – Sanatocin Arewa

Date:

Kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya ta ce ba ta goyon bayan amfani da karfin soji don tilasta wa sojojin Nijar mayar da mulki ga hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

Mai magana da yawun ƙungiyar, Sanata Abdurrahman Kawu sumaila ya shaida wa BBC cewa, duk da cewa sanatocin ba su goyi bayan juyin mulkin da sojojin na Nijar suka yi ba, to amma kuma ba su goyi bayan amfani da karfin soji da ƙungiyar Ecowas ke shirin ɗauka kan Nijar din ba.

”Muna so ne a yi amfani da hanyoyin diplomasiyya wajen warware wannan matsala, amma ba ƙarfin soji ba”, in Sanata Kawu Sumaila.

Ya ƙara da cewa ƙungiyarsu tana la’akari da kusancin Nijar da Arewacin Najeriya

“‘jihohin Najeriya kusan guda bakwai duk sun yi iyaka da Nijar kuma kusan duka waɗannan jihohi, akwai matsalolin tsaro, kama daga na Boko-Haram zuwa na ‘yan fashin daji”.

”Idan muka bari aka fara yaƙi tsakanin Najeriya da Nijar to masifar da Najeriya za ta shiga, ita kanta Nijar dinma ba za ta shiga wanna masifa ba”, in ji Sanatan da ke wakilar Kano ta Kudu.

Sanata Kawu Sumaila ya ce hakan zai sa ‘yan ta’addan take waɗannan yankuna su ƙara samun dama wajen ci gaba da ɓarnar da suke gudanarwa.

Ya ƙara da cewa ”kuma yanzu halin da talakawan ƙasar nan ke ciki na matsin rayuwa da sauran matsaloli, idan aka fara yaƙin gaskiya yankunan Najeriya da ke iyaka da Nijar za su sake shiga cikin wata masifa”.

A ranar Juma’a ne shugaban Najeriya Bola Tinubu, kuma shugaban Ecowas, ya aike wa Majalisar Dattawan Najeriya buƙatar amincewarta domin tura sojojin ƙasar zuwa Jamhuriyar Nijar.

taraba news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp