Jam’iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya ta yi watsi da sakamakon zaɓen cike gurbi na ɗanmajalisar jiha da aka gudanar a mazaɓar Ghari da Tsanyawa.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Lahadi, shugaban NNPP na Kano Hashim Dungurawa ya zargi abokan hamayya da haɗa kai da jami’an hukumar zaɓe domin “aikata maguɗi”.
Hukumar zaɓe ta ayyana APC mai adawa a jihar ce ta samu nasara a zaɓen da aka gudanar a jiya Asabar, yayin da kuma aka doke ta a ɗaya zaɓen na mazaɓar Bagwai/Shanono – wanda ta nemi a soke ita ma.
“An gudanar da zaɓe a rumfuna 10 na ƙaramar hukumar ta Ghari lafiya, amma kuma wasu ‘yansiyasar APC sun haɗa kai da jami’an hukumar zaɓe wajen sanar da ɗantakarsu a matsayin wanda ya yi nasara,” in ji shi.
Jam’iyyar ta kuma soki hukumar zaɓe saboda “sanar da sakamakon a hedikwatarta ta jiha” maimakon “cibiyar tattara sakamako”.