fidelitybank

Ba mu taba tunanin dage zabe ba – INEC

Date:

Shugaban Hukumar Zaɓe ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya jaddada shirinsu na gudanar da babban zaɓe na 2023 a lokacin da aka tsara, yana mai cewa “ba mu taɓa tunanin ɗage zaɓen ba”.

Hukumar ta tsara gudanar da zaɓen daga ranar 25 ga watan Fabarairu mai zuwa, inda za a zaɓi shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya, daga baya kuma a zaɓi gwamnoni da ‘yan majalisar jiha a watan Maris.

Sai dai yayin wani taro a farkon makon nan, wani babban jami’in Inec ya bayyana cewa idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba matsalolin tsaro za su sa a ɗaga zaɓen a wasu yankunan Najeriya.

“Inec ba ta da wani tunanin sauya jadawalin zaɓen ballantana ma ɗage shi. Irin tabbacin da jami’an tsaro suka ba mu na tsaron lafiyar ma’aikatanmu ya ƙarfafa mana gwiwar ci gaba da shirye-shiryenmu,” in ji farfesan a ranar Laraba.

Ya ba da tabbacin ne yayin da ya gana da jam’iyyun siyasa 18 da za su fafata a zaɓen, inda ya gabatar musu da kundin rajistar masu kaɗa ƙuri’a da yawansu ya kai miliyan 93.4.

“Babban zaɓen 2023 zai gudana yadda muka tsara shi. Duk wani rahoton da ya ruwaito saɓanin haka ba matsayarmu ba ce,” kamar yadda ya jaddada.

sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hogan ya mutu bisa cutar gazawar koda

An bayyana cikakkun bayanai game da mutuwar ɗan wasan...

Sojoji sun kashe rikaken dan Bindiga Dan Dari Biyar a Sokoto

Dakarun Operation FANSAR YANMA sun yi nasarar fatattakar wani...

An kashe utane 30 a yakin Thailand da Cambodia

An shiga kwana na uku na faɗan kan iyaka...

Ba mu ƙayyade shekarun shiga ƙaramar sakandare JSS1 – Ma’aikatar Ilimi

Ma'aikatar Ilimi a Najeriya ta musanta rahoton da wasu...

Ido da Ido na ga yadda Sojojin Isra’ila ke kashe Falasdinawa – Tsohon Sojin Amurka

Wani tsohon sojan Amurk ya ce, ya ga yadda...

‘Yan majalisar Birtaniya 220 na neman ƙasar ta amice da ƙasar Falasɗinu

'Yan majalisar Birtaniya 220 sun nemi gwamnatin ƙasar ta...

Buhari yaki karbar kyautar Agogon lu’u-lu’u da jirgin sama – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari,...

An kama wanda ya kashe tsohuwar Matarsa a Jigawa

Ƴansandan Jihar Jigawa sun ce, sun kama wani mutum...

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan Kwankwaso

Fadar shugaban kasa, ta mayar wa tsohon gwamnan Kano...

Barau FC ta naɗa Ladan Bosso sabon kocinta

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta sanar da...

Am fara dawo da ‘yan Najeriya daga Afrika ta Tsakiya

Hukumomi a Najeriya sun ce, sun fara ƙoƙarin mayar...

G-Fresh da Hamisu Breaker sun samu gurbi kurkuku bayan sun watsa Naira

Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ɗaure shahararrun...
X whatsapp