Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta kwatanta ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da cewa abu ne da ba a yi tsammanin afkuwarsa ba.
Ambaliyar ta afku ne bayan ɓallewar madatsar ruwan Alau, inda ta lalata dubban gidaje tare da ɗaiɗaita mutane da dama.
“Ba mu yi tsammanin ambaliyar za ta kai muni haka ba,” kamar yadda Ezekiel Manzo mai magana da yawun NEMA ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Manzo ya kwatanta ambaliyar da babban bala’i, inda ya kuma ɗora alhakin haka kan sauyin yanayi.