Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC ta ce, ba ta san dalilin da ya sa wasu ‘yan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga ba.
Yayin da yake jawabi a taron manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron ƙungiyar a Abuja, babban birnin ƙasar, shugaban ƙungiyar – wanda shi ne gwamnan jihar Imo, Hope Udozinma – ya ce ”mu ba mu san dalilin da ya sa suke shirin yin zanga-zangar ba, inda mun sani za mu gayyace su don zama da su domin samun maslaha”.
“Mu a matsayinmu na jagorori muradinmu shi ne haɗin kan ƙasar nan, muna maraba da duk wani abu da zai kawo wa ƙasarmu da al’umarmu ci gaba ta hanyar samar da ayyukan yi ga matasa maza da mata da ke kammala karatu”, in ji shugaban gwamnonin na APC.
Uzodinma ya ƙara da cewa rashin wayewa ne a ce za a shirya zanga-zanga a Najeriya a wannan hali da ake ciki, yana mai kira ga ‘yan ƙasar da su kaurace wa yunƙurin zanga-zangar.
Gwamnan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya su yi wa gwamnati haƙuri, yana mai cewa gwamnati na iya bakin ƙoƙarinta don magance matsin tattalin arzikin da ƙasar ke fama da shi.


