Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce Har yanzu ba ta raba muƙamai a majalisa ta 10 ba kamar yadda ake yaɗa wa a shafukan sada zumunta.
Jam’iyyar ta ce zuwa yanzu ba ta keɓe wani muƙami zuwa ga wani shiyya na ƙasar cikin shiyoyyi shida da tae da su, musamman ma na majalisar tarayya ta 10 da ake shirin kafawa.
Cikin wata sanarwa da APC ta fitar jiya Alhamis wanda ya samu sa hannun sakataren hulɗa na ƙasa Felix Morka, ta ce bayanin da ake yaɗa ba daga gare ta ya fito ba, don haka ta ce mutane su yi wasi da shi.
APC ta ce za ta fitar da sanarwa kan matakin idan har bukatar hakan ta taso.