Gwamnatin jihar Kano, ta ce ba ta kori ma’aikata 10,800 da aka dakatar da albashin watan Yuni ba.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ma’aikatan 10,800 ne gwamnatin tsohon gwamna, Dakta Abdullahi Ganduje ta dauka aiki.
Bayanin hakan ya fito ne a ranar Juma’a a Kano a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Baba Dantiye ya yi; Akanta Janar Abdukadir Abdulsalam, da Shugaban Ma’aikata (HOS), Usman Bala-Muhammad.
Hukumar ta HOS ta bayyana cewa ba a kori ma’aikata 10,800 ba, sai dai an daina biyansu albashi har sai an tantance matsayinsu.
“Bari in bayyana sarai cewa babu wani ma’aikaci da aka kori. An dakatar da albashinsu don tsaftace tsarin saboda wasu zarge-zarge.
“Ba da jimawa ba za a kafa kwamitin tantancewa kuma bayan an kammala aikin wadanda aka dauka bisa ka’ida ta hanyar ka’idojin aikin gwamnati za su karbi albashinsu.”