Amurka ta ce gwamnatin Nijar ta musanta umartar jakadiyar ƙasar ta gaggauta ficewa daga kasar a lokacin da ta kai ziyara Nijar din a kwanakin baya.
Wasu wasiƙu da aka gani a shafin intanet – da wasu jami’an gwamnatin Jamhuriyar Nijar din suka aika wa jakadojin Amurka da Faransa da Jamus da Kuma Najeriya masu alamun ban hakuri ne – suka tabbatar da hakan.
Tun da farko ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta sanar da cewa sojojin – da suka yi juyin a Nijar din cikin watan da ya gabata – ba su da ikon korar jakadanta da ke ƙasar.


