fidelitybank

Ba mu kashe ƙananan yara ba a rangwame mu da ƴan Boko Haram – Sojoji

Date:

Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ƙaryata rahotonni da ke zargin dakarun sojoji da kashe ƙananan yara a yaƙin da rundunar ke yi da mayaƙan Boko Haram a arewa maso gabas.

A watan Disamban bara ne kamfanin dillancin labarai na Reuters a wani rahoton bincike da ya fitar ya zargi sojojin Najeriyar da gudanar da wani shiri a asirce na zubar wa da aƙalla mata 10,000 ciki.

Waɗanda suka kuɓuta daga hannun mayaƙan Boko Haram a yankin arewa maso gabshin ƙasar.

Karanta Wannan: Sojoji sun yi rugu-rugu da ƴan Boko Haram a Bama

Rahoton ya ce tun a shekarar 2018, sojojin Najeriya ke gudanar da shirin a asirce na zubar wa da matan ciki ba bisa ƙa’ida ba a yankin.

Lamarin da rahoton ya ce ya sa an zubar wa da mata akallan 10,000 ciki tsakanin manyan mata da ‘yan mata, waɗanda mayakon Boko Haram suka yi wa fyade bayan yin garkuwa da su.

Rahoton dai ya ja hankalin ƙasashen duniya, inda babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga gwamnati da ta gudanar da gagarumin bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace don hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.

To sai babban hafsan sojin ƙasa Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ce sojojin Najeriya na ɗaya daga cikin rundunonin soji mafi inganci a faɗin duniya, wadanda ya ce suna gudanar da ayyukansu ta hanyar bin doka tare da kare ‘yancin ɗan adam.

Yayin da yake magana a wajen ƙaddamar kwamitin bincike na musamman kan tauye haƙƙin ɗan adam a lokacin yaƙi da ta’addanci na yankin arewa maso gabashin ƙasa da aka yi wa laƙabi da (SIIP-North East).

Janar Yahaya ya ce ”dakarun sojin ƙasar ƙwararrun dakaru ne waɗanda ke aiki bisa turbar doka, kuma ƙarƙashin zaɓaɓɓiyar gwamnatin, inda shugaban ƙasa da sauran hukumomin tsaro duka suke nan, don martaba doka, duka mun san wannan.”

Yayin da yake ƙaryata rahoton zubar wa da matan cikin, Janar Yahaya ya zargi kamfanin dillancin labaran da rashin bayyana haƙiƙanin abin da ke faruwa na mamayar da sojojin suka yi ƙungiyar a shekarun baya-bayan nan.

Ya ƙara da cewa yankunan da rahoton ya ambato cewa an aikata wannan laifi, wurare ne da ke cikin matsanancin tsaro, waɗanda ake buƙatar rakiyar soji kafin shiga cikinsu.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp