fidelitybank

Ba mu karya doka ba a sababbin kuɗi – CBN

Date:

Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya ce, ya bi doka da ƙa’ida wajen sauya fasalin takardun kuɗin ƙasa uku da yake shirin yi.

Kakakin CBN, Mista Osita Nwanisobi, na mayar da martani ne ga Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna Ahmed, wadda ta ce ba a tuntuɓi ma’aikatarta ba kafin aiwatar da sauyin.

Da take magana lokacin da ta bayyana a gaban wani kwamatin Majasliar Dattawa ranar Juma’a, Zainab ta soki shirin tana mai cewa “ba lokacin da ya dace ba ne”.

Sai dai Mista Nwanisobi ya ce, hukumomin CBN sun bi ƙa’ida wajen neman amincewar Shugaba Buhari kamar yadda sashe na 2(b) da sashe na 18(a) da sashe na 19(a) (b) na dokar CBN ta 2007 suka tanada don neman sauya fasali da samarwa da fara aiki da kuma yaɗa sabbin takardun kuɗi na N200 da N500 da N1,000.

A ranar Laraba ne babban bankin ya ba da sanarwar sake takardun na naira, inda ya ce kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen ƙasar na hannun mutane maimakon bankunan kasuwanci.

CBN ya bai wa ‘yan ƙasar wa’adin kwana 42 da su mayar da kuɗaɗen ga bankunan kasuwanci kuma yana sa ran nan da 15 ga watan Disamba mai zuwa zai fitar da sabbin takardun N200 da N500 da N1,000

nigerianewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...

NNPP ta yi tafka magudi a zabencike gurbin Kano – Farouk Lawan

Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin...

Dan shugaban kungiyar Boko Haram ya shiga hannu

Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar...

Daga yau wankin koda a Najeriya ya koma dubu 12 maimakon dubu 50 – Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya amince da rage farashin...

An ceto Mutane 25 da syka kife a kwale-kwalen Sokoto

Hukumomi a jihar Sokoto sun ce, sun samu nasarar...

An fara duba rabon gyaran arzikin Najeriya

Shugaban Hukumar rarraba arziƙin ƙasa RMAFC, Mohammed Shehu, ya...
X whatsapp