Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), ya musanta rahotannin da ke cewa ya kara kudin tallafin man fetur da sama da naira tiriliyan uku a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun kamfanin na NNPCL, Olufemi Soneye, ya jaddada cewa an tabbatar da ikirarin tallafin da kamfanin ya bayar, tare da mika dukkan bayanan da suka dace ga hukumomin da suka dace.
Ya kuma bayyana cewa kamfanin na NNPCL bai san wani shiri na tantance asusun ajiyarsa ba, kamar yadda rahotannin kafafen yaÉ—a labarai na farko suka nuna.
“NNPCL ta lura da wani rahoto a wani sashe na kafafen yada labarai da ke zargin cewa ta kara kudin tallafin da naira triliyan 3.3,” in ji Soneye.
“NNPCL tana gudanar da kasuwancinta ne cikin gaskiya bisa kyawawan halaye na Æ™asashen duniya, kuma ba ta taÉ“a Æ™ara wani kuÉ—in tallafi man fetur ba ga Gwamnatin Tarayya.” in ji sanarwar
“Duk da’awar tallafin da aka yi a baya ana iya tabbatar da su, tare da rubuce-rubuce da takardu da aka aika ga hukumomin da abin ya shafa.” Sanarwar ta Æ™ara haske.
Kamfanin ya kuma jaddada Æ™udirinsa na yin aiki bisa tsarin kasuwanci a Æ™arÆ™ashin dokar masana’antar man fetur tare da bayyana cewa zai bijire wa duk wani yunÆ™uri na siyasantar da batun tallafin man fetur.
Sanarwar ta Æ™ara da cewa “NNPCL ta gayyato masu binciken kuÉ—i na waje don yin bitar littattafanta a lokuta da dama.”