fidelitybank

Ba mu kara farashin man fetur ba – Gwamnatin Tarayya

Date:

Gwamnatin tarayya ta musanta yin ƙarin farashin man fetur, duk kuwa da ƙaruwar farashin man a faɗin ƙasar.

Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ambato ƙaramin ministan albarkatun man fetur na ƙasar Timipre Sylva a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ta hannun mai taimaka masa kan kafofin yaɗa labarai, cewa Shugaban ƙasar bai amince da wani ƙarin sabon farashi ga man fetur ɗin ba.

A ranar Juma’ar ne dai shugaban masu gidajen mai masu zaman kansu reshen Jihar Kano Bashir Danmallam ya tabbatar wa BBC da ƙarin farashin man fetur ɗin da kashi 8.8 cikin 100, inda ya ce sun samu umarni daga gwamnatin tarayya.

To sai dai sanarwar da ƙaramain ministan man fetur ɗin ya fitar ta ce ”babu wani dalili da shugaban ƙasar zai amince da ƙarin farashin man a daidai wannan lokaci”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ”gwamnati ba za ta amince da ƙarin farashin man fetur a asirce ba, ba tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a fannin man fetur din ba”.

”Dan haka shugaban ƙasa bai umarci ƙungiyar dillalan man fetur da cewa su ƙara kuɗin man fetur ɗin ba”, in ji sanarwar

Haka kuma sanarwar ta ambato ministan na yin kira ga ‘yan ƙasar da su kwantar da hankulansu, su kuma zama masu bin doka, a yayin da gwamnatin ƙasar ke iya bakin ƙoƙarinta wajen wajen dawo da al’amuran rarraba man kamar yadda aka saba a baya.

Tun cikin watan Oktoban bara ne dai ake fuskantar ƙarancin man fetur a wasu sassan ƙasar, lamarin da ya haddasa sayar da man a mabambantan farashi a sassan ƙasar wadda ta fi kowacce ƙasa arzikin man fetur a nahiyar Afirka

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp