fidelitybank

Ba mu kama Dan Jaridar da ya yi hira da abokan hamayya ba – Gombe

Date:

Gwamnatin jihar Gombe ta musanta bayar da umarnin kama wani dan jarida a gidan rediyo, saboda karbar bakuncin wani dan jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) kamar yadda jam’iyyar ta yi zargin.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Alhaji Shuaibu Gara, mai ba Gwamna Inuwa Yahaya shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru kuma ya bayyanawa manema labarai a Gombe ranar Lahadi.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, ta tuna cewa, wani dan jarida da ke aiki da Jewel FM Gombe, tare da bakon sa, ‘yan sanda sun kama shi tare da tsare shi bayan shirya wani shiri.

“Abin da muka sani shi ne gwamnati ta kai karar ‘yan sanda cewa, mun sanya ido a kan wani shiri na mintuna 30 na rediyo inda aka gayyaci bako zuwa shirin siyasa.

“Kuma a cikin shirin, bakon ya yi zargin cewa gwamnati ta kashe Naira biliyan 4 don katangar gidan gwamnati.

“Mun gabatar wa ‘yan sanda bayanan mu na kasafin kudin jihar baki daya don kula da duk wasu gine-ginen gwamnati tsakanin 2019 zuwa 2022. Don mu yi masa adalci mu ma muna son ‘yan sanda su nemi ya ba shi shaidarsa.

“Ta yaya wani zai ce mun kashe sama da Naira biliyan 4 don kawai katangar gidan gwamnati kadai.

“Idan aka fuskanci masu bincike, wanda ake zargin bai ma san adadin miliyan nawa ya kai Naira biliyan 1 ba,” in ji shi.

Ya kuma kalubalanci ‘yan adawa da su bayar da hujjar cewa an kama duk wani dan jarida, inda ya kara da cewa gwamnati kawai ta gabatar da kara ga ‘yan sanda a kan bakon gidan rediyon da ya yi zargin rashin gaskiya a kan gwamnati.

“Gwamnatin Gombe ba ta bayar da umarnin kama wani dan jarida ba, duk wanda ya ce an kama dan jarida, to dan jaridan ya nuna mana amincewar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ),” inji shi.

Gara ya kuma yi kira ga jama’a masu son samun duk wani bayani daga gwamnati da su bi hanyoyin da suka dace.

nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp