fidelitybank

Ba mu ga dalilin sauya matsayinmu ba akan shiyya-shiyya – PDP

Date:

Gwamnonin jam’iyyar PDP na Kudancin Najeriya sun dage cewa, ya kamata jam’iyyar ta tsayar da tikitin takarar shugaban kasa a 2023 zuwa yankin kudanci, domin yin gaskiya da adalci.

Gwamnonin jam’iyyar adawa, sun bayyana matsayarsu kan batun shiyya-shiyya yayin da suke zantawa da manema labarai bayan ganawar da suka yi a daren Juma’a a masaukin Gwamnan Akwa-Ibom, Asokoro, Abuja.

Gwamnan jihar Abia, Dr Okezie Ikpeazu, wanda ya yi magana a madadin gwamnonin, ya ce, sun sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar PDP dangane da shiyya-shiyya, amma ba su da dalilin sauya matsayarsu a baya.

“Matsayinmu shi ne na farko, mun jajirce wajen hadin kan jam’iyyarmu, kuma mun yi aiki tukuru don ganin cewa, jam’iyyar ta ci gaba da kasancewa mai karfi da kuma abin dogaro don ‘ceto’ Najeriya a 2023.

“Ko ma dai, muna so mu ja hankalin ku kan yadda muka amince a matsayinmu na gwamnonin Kudancin Legas da kuma a Delta cewa jam’iyyar ta mutunta ka’idar shiyya-shiyya kamar yadda kundin tsarin mulkinmu ya tanada.

“Saboda haka, muna jin cewa abin da ya fi dacewa a yi shi ne shiyyar shugabancin kasa zuwa Kudu, kuma mun tsaya kan wannan matsayi.

“Ba mu ga dalilin sauya matsayinmu ba, domin an kafa jam’iyyar ne bisa adalci da gaskiya.

“Muna kuma tunanin cewa, adalci da gaskiya sune ginshiƙai masu mahimmanci waɗanda za su daidaita siyasarmu zuwa tafiyarmu na ceto Najeriya,” in ji Ikpeazu.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp