fidelitybank

Ba mu fara neman Matawalle ba tukuna – EFCC

Date:

hi

Hukumar da ke yaƙi da yi wa arziƙin ƙasa ta’annati EFCC ta ce ba ta neman tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ruwa a jallo.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter EFCC ta ce ta fitar da wannan sanarwar ne bayan jan hankalinta da aka yi kan rahoton wata jarida da ta wallafa a ranar Lahadi 18 ga watan Yunin nan da muke ciki da ke cewa tana neman Matawalle ruwa a jallo.

“Hukumar EFCC ta ayyana Matawalle a matsayin wanda take nema ruwa a jallo ta kuma nemi hukumar tsaro ta fararen kaya DSS ta kama shi “duk inda aka ganshi”, kamar yadda jaridar ta bayyana, in ji sanarwar.

EFCC ta ce rahoton ba daidai ba ne, ya zuwa yanzu ba ta ayyana Matawalle a matsayin wanda take nema ba, ko neman DSS ta kama mata shi.

Sanarwar ta ƙara da cewa Hukumar na da tsarin da take bi wajen ayyana mutum a matsayin wanda take nema, kuma tana da hanyoyin da take bi ta sanar da mutane tana neman shi, ba ta hanyar amfani da majiyoyin bogi ba.

A baya-bayan nan dai an yi samun takun saka tsakanin tsohon gwamnan na jihar Zamafar da hukumar ta EFCC, inda Matawallen ya zargi tsohon shugaban Hukumar Abdurrasheed Bawa da tafka almundahana iri-iri.

A makon da ya gabata ne dai shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar Abdurrasheed Bawa.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta ce shugaban ƙasar ya ɗauki matakin dakatar da Bawa ne domin bayar da damar gudanar da bincike kan wasu manya-manyan zarge-zargen da ake yi masa.

breaking news in nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp