fidelitybank

Ba mu fara amfani da dokokin shari’ar musulunci ba wajen yin hukunci – FRSC

Date:

Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadurra ta Kasa FRSC, ta nesanta kanta da wani labari da ke cewa hukumar na shirin fara amfanin da dokokin shari’ar musulunci wajen hukunta masu karya dokokin tuƙi da amfani da hanya

A cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Bisi Kazeem, aka kuma wallafa a shafin hukumar na Tuwita , ta ce wannan labari ba shi da alaƙa da hukumar.

A cikin makon da ya gabata ne dai wasu jaridun ƙasar suka ruwaito wani kwamandan hukumar reshen wata jiha a ƙasar na kira da fara amfani da dokokin shari’ar musulunci ga masu karya dokokin tuƙi a ƙasar.

Yana mai cewa dokokin hukumar sun gaza ta fuskar hukunta masu laifukan, a don haka ne yake kira da hukumar ta fara amfani da dokokin shari’ar musulunci.

To sai dai a sanarwar hukumar ta fitar, ta ce babban kwamandan hukumar na ƙasa Dauda Ali Biu ya umarci kwamandan da ya yi wannan furuci da ya hallara a shalkwatar hukumar da ke Abuja, domin a cewar sanarwar kalaman nasa sun saɓa dokokin hukumar.

Sanarwar ta ce dokoki da ƙa’idojin da suka kafa hukumar ba dokoki ba ne na wani addini ko wani yanki na ƙasar.

A don haka hukumar ke kira ga al’umma da su yi watsi da furucin da jami’in ya yi , tana mai cewa ya saɓa wa dokoki da ƙa’idojin hukumar

daily post nigeria today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...
X whatsapp