Kamfanin samar da man fetur na NNPCL, ya bai wa masu sayen mai a gidajen man fetur dinsa cewa ba shi da niyyar kara kudin litar mai.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X tsohon shafin Tuwita, NNPC ya ce sabanin rade-radin da ake yi na karin farashin litar mai a kasar, masu sayen man fetur na iya ci gaba da shan mai a gidan man fetur dinsa da ke fadin kasar a cikin farashin mafi rahusa.
Sanarwar NNPC na zuwa daidai lokacin da wasu kafofin yada labaran Najeriya ke cewa farashin litar mai a tashoshin sauke man fetur na kasar, ya kai naira 720 duk lita daya, abin da ya sa ake jin farashin zai iya kai wa naira 729 a gidajen mai matukar gwamnatin kasar ba ta ci gaba da biyan kudin tallafi ba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa harkoki sun tsaya a tashoshin sauke man fetur, yayin da a wasu wurare, wasu gidajen man fetur suka rufe.
Wasu direbobin mota a birane kamar Abuja da Kano sun ba da rahotannin cewa sun sha mai a farashin da ya haura abin da aka saba sayarwa a baya.