Gwamnatin jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya ta yi karin haske game da bayanin da ta nema ga Masarautar Katsina na rashin halartar wasu hakimai hawan bikin Sallah.
Gwamnatin ta nemi bayanin ne a cikin wata takarda da ta aika wa masarautar Katsina mai dauke da umarnin gwamnan jihar.
A nata bangaren, Masarautar Katsina ta tabbatar da samun takardar, kuma ta ce tana shirin bai wa gwamnatin amsa.
Ga karin bayani cikin rahoton Awwal Ahmad Janyau.