Ƙungiyar makiyaya ta Gan Allah Fulani Development Association (GAFDAN), ta musanta zargin fulani da hannu a kashe-kashen da aka yi na kwana-kwanan nan a jihar Filato.
Shugaban ƙungiyar, Garba Abdullahi ne ya ƙaryata zargin, inda ya ce an ƙirƙira maganar ce domin a ɓata sunan fulani.
“Muna jajanta wa waɗanda suka rasa ƴanuwansu, kuma muna Allah wadai da kashe-kashen. Dabbanci ne, kuma bai dace ba. Amma mu fulani muna faɗa da babbar murya cewa zargin ƙungiyar ci gaban al’adun mutanen Bokkos babu tushe, zargin da suke yi na fulani na da hannu a kisan shaci-faɗi ne kawai.
“Muna kira ga ƴan Najeriya da gwamnati da jagororin al’umma da su yi watsi da wannan zargin, domin babu hannun al’ummar fulani a ciki.”