Iran “ba ta da hannu” cikin harin da Hamas ta kai kudancin Isra’ila, in ji ofishin jakadancin Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya.
“Muna jaddada goyon bayanmu ga Falasɗinawa; amma duk da haka ba mu da hannu a matakin da Falasɗinawa suka ɗauka, saboda su ne suka ɗauki matakinsu da kansu,”kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wata sanarwa da suka fitar ta fada.
Tun da fari Hamas ta ce ta kai harin ne da taimakon Iran a cikin ƙarshen makon.
Iran dai ta jima tana goyon bayan Hamas na tsawon shekaru kuma tana bai wa mayakanta makamai da horo.
Sai dai sakataren harkoki wajen Amurka Antony Blinken ya shaida wa CNN a ranar Lahadi cewa Gwamnatin Amurka “ya zuwa yanzu ba ta samu wata shaida da ke nuna cewa Iran na da hannu cikin wannan rikin”.