Gwamnatin jihar Abia ta musanta zargin da aka yi mata na kokarin korar al’ummar arewa daga jihar, bayan yunƙurinta na sauya fasalin kasuwar dabbobi ta Lokpana da ke kan hanyar umuahia zuwa Aba, a jihar.
A ranar Litinin ne shugabannin kasuwar ta Lobbanta da ke ƙaramar hukumar Umunneochi suka gana da manema labaru a birnin Kaduna, inda suka buƙaci shugaban ƙasa da mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya su tsoma baki domin dakatar da gwamnatin jihar daga shirinta na tayar da kasuwar.
Sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta ba su mako biyu su tashi daga kasuwar duk kuwa da cewa sun kasance masu bin doka da oda.
Sai dai a cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta hannun sakataren yaɗa labarun gwamnan jihar, Kazie Uko, ta ce batun sauya fasalin kasuwar ya taso ne bayan wasu rahotannin tsaro da suka tabbatar da cewa kasuwar ta kasance maɓuya ga ƴan fashi da masu garkuwa da mutane a cikin shekarun da suka gabata.
A cikin wani bayani da ya yi wa manema labaru ranar Litinin, mai bai wa gwamnan jihar shawara kan tsaro, Navy Commander Macdonald Ubah, mai murabus, ya ce sauran ayyukan laifi da ake zargin ana aikatawa a kasuwar sun haɗa da sayar da sassan jikin bil’adama da kuma faɗace-faɗace.
Ya ƙara da cewa ana amfani da kasuwar wajen karɓar kuɗin fansa na mutanen da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Uturu zuwa Umunneochi.
Ya ce wannan lamari ne ya sanya gwamnatin jihar ta ɗauki matakin rushe gidajen mata masu zaman kansu da rumfunan da aka gina ba bisa tsari ba a kasuwar.
Sanarwar gwamnatin jihar ta ce matakin da ake son a ɗauka shi ne kawar da wuraren kwana a kasuwar tare da mayar da ita wadda za ta rinƙa ci da rana kawai.
Ta ƙara da cewa kuma gwamnati ba za ta janye aniyar tata ba ta sauya fasalin kasuwar.
Sanarwar ta kuma musanta zargin da ake yi na cewa gwamnatin jihar na ƙoƙari ne wajen korar al’ummar arewa daga jihar.


