fidelitybank

Ba mu amince da bashin da Tinubu zai baiwa ɗalibai ba – ASUU

Date:

Kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa  (ASUU), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sauya dokar ba da bashin karatu ga dalibai da ya amince da ita, zuwa tallafin karatu domin bai wa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi damar samun ilmi mai zurfi.

A wata hira da gidan Talbijin na Channels ranar Lahadi, shugaban ASUU ya ce bashin karatun ba abu ne mai yiwuwa ba. A cewarsa, bayar da bashi don yin karatu “ba zai dore ba”.

Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, “tunanin bayar da bashin karatu ga dalibai ya zo ne a 1972 kuma yana cikin harkokin bankuna da aka kafa”.

Ya yi iƙirarin cewa mutanen da suka karɓi bashin, ba su taɓa biya ba, kuna iya zuwa ku bincika. A shekarar 1994 ko 1993, sojoji sun kafa dokar soja mai lamba inbda suka kafa hukumar bayar da bashi ga ɗalibai. Sai Majalisar dokoki ta daidaita ta a shekara ta 2004 kuma a cikin shekara ɗaya, ta wargaje. Kuɗaɗen suka bace. Muna so mu ga yadda wannan zai bambanta”.

A cewarsa, akwai dalibai sama da miliyan daya a jami’o’in gwamnatin Najeriya kuma rancen ba zai iya biyan kudin karatun dalibai ba.

A ranar Litinin ne Shugaba Tinubu ya sa hannu a kan dokar ba da bashi ga dalibai domin cika alƙawarin da ya dauka a lokacin yaƙin neman zabensa.

Shugaban majalisar wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila, wanda yanzu shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ne ya dauki nauyin gabatar da ƙudurin dokar a majalisa.

Dokar ta tanadi ba da bashi maras ruwa ga daliba masu ƙaramin ƙarfi a Najeriya

vanguard news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp