Ma’aikatar Ilimi a Najeriya ta musanta rahoton da wasu jaridu suka ruwaito cewa gwamnatin ƙasar ta ƙayyade shekara 12 a matsayin shekarun da yara za su shiga ajin farko na ƙaramar sakandare wato JSS1.
Cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, mai magana da yawun ma’aikatar Folasade Boriowo ta ce “baki ɗayan rahoton ba daidai ba ne”.
“Domin kore wani shakku, mafi ƙanƙantar shekarun shiga JSS1 yana nan a 10,” in ji ta. “Bisa doka, babu yaron da zai kammala firamare a ƙasa da shekara 10.”
Sanarwar ta ƙara da cewa rahoton bai samo asali daga kowace irin majiyar hukuma ba, sannan kuma Ministan Ilimi Tunji Alausa ya nanata sabon tsari na shekara 16 a matsayin mafi ƙanƙanta kafin shiga jami’a a Najeriya.