fidelitybank

Ba ma tsoron zuwa kotu a Kano – NNPP

Date:

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano, ta mayar wa APC mai barin gado martani game da kiraye-kirayen da take yi cewa hukumar zabe ta sake nazari kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ya bai wa Abba Kabir Yusuf (Gida-gida) nasara a zaben da aka yi da ya ba shi nasara.

APC dai ta ce ba ta amince da sakamakon zaben ba, kuma za ta garzaya kotu don ƙalubalantar sa.

To, sai dai shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Umar Haruna Doguwa ya ce duk masu bai wa Dr Nasiru Yusuf Gawuna shawarar ya je kotu to kuwa so suke ya yi biyu babu.

A hirarsa da wakilin BBC a jihar Kano, Doguwa ya ce ko a jikinsu indai kan batun garzayawa kotu ne, ”Wallahi ko gezau ba mu yi ba, aje kotun mun tabbatar mu na da nasara an yi sahihin zabe, dan haka ba za mu hana kowa zuwa kotu ba.”

Karanta Wannan: Zamu ladabtar da ‘yan siyasan dake tinzira magoya bayansu

Ya ce takarar nan ba shi ne na farko ba, dukkan zabukan da aka yi NNPP ta na rinjaye a jihar Kano, kuma a bayyane ta ke kowa ya san APC ba ta da wani tasiri.

Doguwa ya ce ”ko gezau, ko gezau, ko gezau Abba, babu abin da ya dame mu, aje kotun mun shirya. Mun godewa jama’ar jihar Kano da suka zabi Abba, kwanann nan zai karbi shaidarsa ta cin zaben gwamna. Sannan ba mu damu ko faduwar gaba akan wannan ba, ai Kwankwaso ne jagoranmu don haka ba wani dar,” in ji shi.

Ya kara da cewa duk ma su zuga Dr Nasir Yusuf Gawuna, ingiza mai kantu ruwa su ke yi masa, za su kai shi su baro.

”Masu zuga Gawuna ya je kotu so suke su kai shi su baro, idan an zo batun rabon mukamai a gwamnatin Tarayya, za a duba wadanda suka fadi zaben gwamna ka ga anan Gawuna da Murtala Suke Garo za a duba, amma yanzu idan sun je kotu Tinubu zai ce ban da su saboda ana kotu, anan ka ga babu wanda za a duba sai Ganduje, dan haka ya yi biyu-babu.”

Abba Kabir Yusuf ya yi nasara a zaben gwamna da aka gudar a ranar 18 ga watan Mayun 2023, inda ya kada abokin takararsa na jam’iyyar APC mai mulki kuma mataimakin gwamna Dr Nasiru Yusuf Gawuna.

Sai dai jam’iyyar APC ta ce za ta kalubalanci zaben, bi sa zargin an yi aringizon kuri’u a zaben.

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp