‘Yan wasan Australia sun dage cewa, ba sa tsoron Lionel Messi, yayin da suke shirye-shiryen karawarsu a wasan zagaye na 16 a gasar cin kofin duniya ta 2022.
Duk da haka, sun yarda da sha’awar su ga wanda ya lashe Ballon d’Or sau bakwai.
Ostiraliya ta samu nasarar ne bayan da ta doke Denmark da ci 1-0.
Yanzu haka dai kungiyar kwallon kafa ta Socceroos za ta kara da Messi da abokan wasanta a yammacin ranar Asabar domin samun gurbi a wasan kusa dana karshe.
“A koyaushe ina son Messi kuma ina tsammanin shi ne mafi girma da ya taba buga wasan.
“[Amma] ba abin alfahari ba ne a yi masa wasa domin shi mutum ne kawai, kamar yadda mu duka muke.
“Abin alfahari ne kasancewa a zagaye na 16 na gasar cin kofin duniya. Ko mun buga da Argentina ko kuma da mun buga da Poland, da har yanzu abin alfahari ne mu wakilci Australia a zagaye na 16 na gasar cin kofin duniya,” in ji mai tsaron baya Milos Degenek.