Gwamnatin tarayya ta dage da cewa, tana goyon bayan sake tattaunawa kan shirin jin dadin ma’aikatan jami’o’in, bisa ga hakikanin halin da ake ciki.
Ministan ƙwadago Chris Ngige ya ce, gwamnati ba ta ji dadin tsarin da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ke amfani da shi wajen biyan bukatun ta.
ASUU ta shiga yajin aikin gargadi na wata daya a ranar 14 ga watan Fabrairu tare da tsawaita wa’adin watanni biyu, bisa zargin gazawar gwamnati na biya musu bukatunsu.
Sai dai Ngige, da yake magana a yayin ganawarsa da kwamitin gwamnatin tarayya a ofishinsa, ya roki kwamitin da ya tabbatar da ya kammala aikinsa cikin makonni shida kamar yadda yarjejeniyar aiki, MOA, ta tanada da kungiyoyin.
Ministan ya kuma shawarci shugabannin kungiyar ASUU da su nemo hanyar da ta dace ta tursasa ma’aikatar ilimi ta tarayya da kuma hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC, da su gaggauta daukar matakin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da gwamnati maimakon gaggauta yajin aiki a duk lokacin da aka samu sabani.