Ƙungiyar ‘yan kwadago NLC ta yi tir da shawarar da Bankin Duniya ya bai wa gwamnatin Tinubu na ƙara farashin man fetur zuwa N750 duk lita ɗaya.
Shugaban NLC Joe Ajaero ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Abuja cikin wata sanarwa da suka fitar da suka yi wa take da : Farashin Bankin Duniya na N750 ga manyan motoci barazana ce ga tattalin arzikin Najeriya”.
Mista Alex Sienaert wanda shi ke jagorantar masana tattalin arzikin Bankin Duniya a Najeriya ya bayar da wannan shawara yayin gabatar da wata maƙala ta hakin da ake ciki kan ci gaban Najeriya na Disamba 2023.
Masana tattalin arzikin sun fahimci cewa har yanzu gwamnatin na ci gaba da biyan tallafin man fetur, hakan ya sa suka bayar da shawarar a ƙara farashin zuwa N750.
Ajaero ya ce ” Ba wani ɓata lokacin mun yi watsi da wannan shawara ta Bankin Duniya wadda ta nemi gwamnatin Najeriya ta ƙara farashin mai zuwa N750 duk lita guda.
“Wannan abin kunya ne, kuma Bankin duniya ya nuna maƙiyin Najeriya ne,” in ji Ajaero.