A ci gaba da kiran gwamnatin rikon kwarya, kungiyar Ohanaeze Ndigbo, koli ta kungiyar al’ummar Igbo, a ranar Litinin, ta sha alwashin goyon bayan zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.
Okechukwu Isiguzoro, Sakatare-Janar na kungiyar Ohanaeze Ndigbo, ya ce kiran gwamnatin rikon kwarya na shaitan ne kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
Isiguzoro ya bukaci hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, da ta kama wadanda ke da hannu a yunkurin kafa gwamnatin wucin gadi.
Isiguzoro ya ce, kungiyar koli ta al’ummar Igbo ba za ta taba shiga cikin irin wannan mugun nufi ba a Najeriya.
A cewar Isiguzoro: “Ndigbo ba zai taba kasancewa cikin kowace gwamnatin wucin gadi ba; kamata ya yi hukumar DSS ta kama wadanda ke bayan fage suna shirin kafa gwamnatin wucin gadi.
“Ohanaeze ta kalubalanci hukumar DSS da ta kama wadanda ke goyon bayan gwamnatin rikon kwarya don tabbatar da cewa marasa kishin kasa na halaka ba su kawo cikas ga dimokuradiyyar mu da mugun nufin hana tafiyar da mulki daga Buhari zuwa Tinubu ba.
Karanta Wannan: INEC maguɗi ta yi ta baiwa Tinubu – Kwankwaso
“Ndigbo zai halarci duk bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu. Muna gargadin wadanda ke aiki a bayan fage ga gwamnatin shege da su yi amfani da kotu wajen bayyana kokensu.
“Muna farin ciki cewa Atiku da Peter Obi sun yi amfani da hanyoyin da suka dace don kwato musu hakkinsu na shari’a. Ba za mu bari ’yan uwa marasa kishin kasa su durkusar da dimokuradiyyar da ake fama da ita a Najeriya ba.
“Ndigbo ya yi Allah wadai da kiraye-kirayen a kafa gwamnatin rikon kwarya a baki da wasiku kuma ya nace cewa za a rantsar da zababben shugaban kasa nan da ranar 29 ga Mayu, 2023.”