fidelitybank

Ba gudu ba ja da baya na cimma buri na – Tinubu

Date:

Shugaban ya kare sauye-sauyen gwamnatinsa, yana mai cewa babu gudu babu ja da baya.

A yayin ganawarsa da wata tawaga daga ƙungiyar kasuwanci ta CCA ƙarkashin jagorancin shugabarta Florizelle Liser, shugaba Tinubu ya jaddada aniyarsa ta ganin ya cimma burinsa na bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da kuma kawo kwanciyar hankali a ƙasar.

A yayin rantsar da shi ne Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur wanda ya kai ga hauhawar farashin man fetur da sauran wasu sauye-sauye da suka janyo darajar kudin ƙasar naira ta yi hasarar darajarta.

Waɗannan sauye-sauyen dai sun haifar da tsadar rayuwa a Najeriya irin wadda ba a taɓa ganin irinta ba abin da ya haddasa zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar da yajin aiki da dai sauransu.

Amma duk da waɗannan ƙalubale da kuma abubuwan da ke faruwa, Tinubu ya ce ba zai ja da baya ba.

“Na yi farin ciki da cewa ƙungiyar CCA na sha’awar sassa daban-daban na tattalin arzikin Najeriya. Muna cikin tsaka mai wuya da fuskantar ƙalubale na sake fasalinmu. Muna da fata, babu shakka, amma ba za mu koma ba,” in ji Tinubu ta bakin mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale.

“Muna fuskantar ƙalubale, kuma mun yi imanin za mu shawo kan waɗannan ƙalubalen. Ina da hali na ‘zan iya cimma wani abu’ wanda dole ne a fassara shi zuwa halin wajibi na cimma abin da nake so’. Muna da tawaga mai kyau da kuma tasiri, kuma dole ne mu ci gaba da mai da hankali don cimma burin da aka sa a gaba,” in ji shugaban Najeriyar.

Tinubu ya sha yin kira ga al’ummar ƙasar da su yi hakuri domin a bar sauye-sauyen nasa su yi tasiri, yana mai cewa za su taimaka wajen jawo jarin ƙasashen waje, amma matakan nasa na ci wa ‘yan Najeriya tuwo a ƙwarya.

Tinubu ya kuma yaba da nasarar da aka samu a kwanan baya na samar da wayar ƙarƙashin teku mai tsawon kilomita 45,000 da ta kawo intanet a jihar Akwa Ibom, wanda zai haɗa yankin Kudu-maso-Kudancin Najeriya da Turai da sauran sassan Afirka.

Shugaba Tinubu ya bayyana muhimmancin wannan nasarar, inda ya bayyana cewa idan aka samar da ingantattun manufofi da haɗin gwiwa da azama, Najeriya za ta iya shawo kan matsalolin da ta daɗe tana fuskanta.

Ya tabbatar da ƙudurinsa na samar da yanayi mai ba da damar kasuwanci don bunƙasa, tare da mai da hankali kan saka hannun jari a muhimman sassa kamar su noma da makamashi da lafiya da fasaha.

“Za mu ƙara kaimi kan harkar tsaro da saka hannun jari a fannin ilimi, domin mun yi imanin cewa ilimi shi ne babban makamin yaƙi da talauci. Muna maraba da abokan hulɗa kamar CCA, kuma za mu ƙarfafa haɗin gwiwarmu don cimma burinmu,” inji shugaban.

A nata martanin, CCA ta bayyana ƙudurinta na tallafawa ci gaban tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyin da gwamnatin shugaba Tinubu ta ba da fifiko.

pulse news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp