Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya ce babu gudu babu ja da baya kan sauye-sauyen da gwamnati mai ci ke yi a bangaren man fetur da iskar gas.
Edun ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin sabuwar ministar kudi Doris Uzoka Anitez a hedikwatar ma’aikatar a ranar Litinin.
“Yanzu Najeriya tana da kudin musaya na kasashen waje wanda ya dogara ne a kasuwa sannan kuma an karya ka’idar farashin kasuwar man fetir wanda gyare-gyare biyu ne da aka dade ana yi a shekaru da dama da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa a halin yanzu.
“Saboda haka a matsayinmu na Ministan Tattalin Arziki na Kasa, mun tsaya kan wata sabuwar alfijir don aiwatar da wadannan sauye-sauye da kara samar da ayyukan yi, samar da ayyukan yi da rage radadin talauci kuma muna farin cikin samun karamin minista da zai taimaka wajen aiwatar da sauye-sauyen da shugaban kasa ya yi. ,” inji shi.
A cewarsa, tuntubar juna da hadin gwiwa muhimmin abu ne wajen cimma wadannan muhimman sauye-sauye daga bangaren gwamnati da masu zaman kansu, yana mai jaddada cewa manufofin tattalin arziki da ake ci gaba da yi na nuna dorewa da kuma alamar nasara.
A nata martanin, Karamar Ministar Kudi ta bayyana kudirinta na yin aiki tare da masu ruwa da tsaki a bangarori masu zaman kansu da na gwamnati don ganin an samu ci gaban tattalin arziki.