Shugaban Amurka Joe Biden, ya dage cewa babu gudu ba ja da baya, wajen ci gaba da takarar shugabancin Amurka duk da kiraye-kirayen da wasu ƴan jam’iyyarsa ta Democrat ke yi na ganin ya hakura.
Mista Biden, mai shekaru tamanin da ɗaya a duniya, ya ce babu wanda zai tursasa masa fasa shiga zaɓen na watan Nuwamba.
Yana magana ne bayan wata ganawa da gwamnonin jam’iyyar Democrat, waɗanda suka jaddada goyon bayansu a gare shi.
Gwamnar Jihar New York Kathy Hochul ta yi ƙarin bayani.
Ta ce mun tattauna kan yadda muka ƙaura daga zamanin da ya yi kama da mulkin sarauta da kama-karya da magabatanmu suka yaƙa, da kuma yadda yanzu, muke fuskantar barazanar sake komawa gidan jiya.
To sai dai Editan BBC a Arewacin Amurka ya ce ƴan jam’iyyar Democrats da dama suna nan cikinsu ya ɗuri ruwa