Gamayyar ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC, ta ce babu gudu ba ja da baya kan yajin aiki da za ta fara daga gobe Talata, 14 ga watan Nuwamban, 2023.
Wata sanarwa da NLC da takwararta ta TUC suka fitar, ta ce an bai wa dukkan rassanta da kuma mambobi ke faɗin jihohi umarnin shiga yajin aikin.
Ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da yin yajin aiki har sai gwamnatoci a dukkan matakai sun yi abin da ya kamata.