Shugaban Amurta Joe Biden ya shaida wa magoya bayansa a jihar ta Wisconsin cewa zai ci gaba da takara babu gudu ba ja da baya, kuma zai doke Donald Trump a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a watan Nuwamba.
Hakan na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da wasu jiga-jigan jam’iyyar Dimokrat ke yi masa cewa ya haƙura da takara, sakamakon rashin tabuka abin kirki a muhawararsa da abokin karawarsa, Donald Trump.
Mutum na baya-bayan nan da ya yi kira shi ne ɗan majalisar wakilai Mike Kali.
To sai dai cikin wani martani da ya mayar a shafinsa na X, Shugaba Biden ya jaddada cewa shi ne cikakken ɗan takarar jam’iyyar.
”Ina son fayyace muku cewa, ni ne shugaban Amurka, kuma ni ne ɗan takarar jam’iyyar Dimokrat, kuma zan ci gaba da takara”.