Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya karyata labarin da aka samu a kwanan baya na cewa an gano tarin zinare a wani yanki na jihar.
Wani rahoton baya-bayan nan ya yi zargin cewa, an gano wani ajiyar zinari da aka kiyasta ya haura tan miliyan 20 da kuma sama da dala tiriliyan 900 a Ehamufu, jihar Anambra.
Sai dai da yake mayar da martani kan wannan ikirari, gwamnan, a wata takardar manema labarai da ya sanyawa hannu a madadinsa, mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaransa, Mista Christian Aburime, ya bayyana labarin a matsayin na bogi.
Labarin ya wuce cewa an gano zinare a Ehamufu ya kuma kara da cewa Soludo, wanda aka bayyana shi a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, ya yi wa manema labarai karin haske kan lamarin.
Da yake daidaita lamarin, Soludo ya ce: “Na farko Ehamufu ba ya jihar Anambra.
“Gwamna Chukwuma Charles Soludo ba shi ne Shugaban kungiyar Gwamnonin Kudu Maso Gabas ba, haka kuma bai yi wa manema labarai karin haske kan duk wani taro da kungiyar ta yi ko kuma ta gano ma’adanar Zinariya a garin Ehamufu da ke Jihar Anambra, kamar yadda marubucin ya yi ikirari. ”
Ya bayyana labarin gaba daya ciki har da duk wata magana da ake dangantawa da Soludo a matsayin karya, yayin da ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da bayanan.