Babban mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan kafofin yaɗa labarai, Temitopr Ajayi ya mayar da martani kan kalaman tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya da ya ce ko ba Tinubu Buhari zai ci zaɓen 2015.
A ranar Laraba ne tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce Buhari ne jigon nasarar APC a 2015 ba Bola Tinubu ba kamar wasu da dama ke iƙirari.
Boss Mustapha ya ce ƙuri’un da APC ta samun zaɓen 2015 an same su ne sakamakon tsantsar farin jinin Buhari.
To amma Temitope Ajayi, ya ce ba don taimakon Tinubu ba, babu ta yadda za a yi Buhari ya ci zaɓen fitar da gwani, ballantana a yi maganar nasara a babban zaɓe.
Ajayi ya ce bai kamata a manta irin ƙoƙarin da Tinubu ya yi ba don tabbatar da Buhari ya zama shugaban ƙasa.
”Mun ji Buhari yana da ƙuri’a miliyan 12 daga jihohin arewa, amma ai duk da haka sau uku yana faɗuwa zaɓen shugaban ƙasa, a 2003 da 2007 da kuma 2011”, in Ajayi.