Ministan kwadago, Chris Ngige, ya ce, da a ce ba kwararre tare da jajirtaccewar Buhari da tuni mulkin Najeriya ya shiga wani hali, da yanzu kasar ta zama tamkar Venezuela.
A cewar ministan yayin da yake karbar lambar yabo da girmamawa ta INSLEC a Abuja, ya ce, da babu Buhari da yanzu ‘yan Najeriya sun tafi gudun hijira a Nijar da Kamaru.
Ministan ya sanar da cewa, duk da kasar nan ta na cikin matsaloli, ba laifin gwamnatin Buhari ba ce, rashin tsarin baya ne yake farautar jama’a.
A cewar The Cable, ministan ya kara da cewa, da babu gogewar mulki irin ta Buhari, da yanzu kasar nan ta kasance cikin rikici kamar Venezuela.