Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya ce da ba a yi taka-tsan-tsan da gwamnonin jam’iyyar ba, da bai zama dan takara ba.
“Kun tsaya min tsayin daka a lokutan bukatu a lokacin gasar firamare ta jam’iyyarmu wanda hakan ya sanya ni zama dan takarar jam’iyyar APC kuma hakan babban abin alfahari ne saboda har yanzu wasu na fafatawa da gwamnoninsu,” inji shi.
A yayin da yake jawabi a wasu tarurrukan da ya yi da Ullama da wasu Fastoci, Tinubu ya jaddada cewa matsayin gwamnoni a kansa ya kara masa kwarin gwiwa da jajircewa wajen yin harbin kan mai uwa da wabi.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, wanda ya yi kaca-kaca da jam’iyyar adawa ta PDP da ta kasa gane bayan shekaru 16 a kan abar shugabanci cewa mulki shi ne babban abin da ke jan ragamar tattalin arzikin kasa, ba shi da wani sabon abu a yanzu.
Ya ce, “PDP ta shafe shekaru 16 tana mulkin kasa amma ta kasa fahimtar cewa mulki shi ne babban abin da zai kawo ci gaban tattalin arziki idan babu wanda zai tafiyar da tattalin arzikin aro wanda ba zai yi wani tasiri ga ‘yan kasarsa ba”.
Tinubu ya tunatar da jam’iyyar PDP cewa a cikin shekaru 16 da suka wuce, sun kashe dala biliyan 16 wajen samar da wutar lantarki, amma har yanzu al’ummar kasar na fuskantar matsalar rashin aikin yi tare da gazawar sadarwa.
Tinubu ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su guji zaben wanda zai basu kulawar kashi 50 cikin 100 sannan ya baiwa Dubai ragowar.