fidelitybank

Ba da yawun mu ‘yan tsohuwar CPC suka goyi bayan Tinubu ba – Malami

Date:

Tsohon Ministan Shari’a na Najeriya, Dakta Abubakar Malami, SAN, ya yi watsi da iƙirarin da wasu ƴan tsohuwar jam’iyyar CPC – da ta narke cikin haɗakar APC – suka yi na nesanta tsohuwar jam’iyyar daga ficewa daga haɗakar.

A farkon makon nan ne wani tsagin tsohuwar jam’iyyar CPC ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Nasarawa, Umaru Tanko Almakura suka yi taro a Abuja, inda suka jaddada goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Tinubu tare da nesanta kansu daga ficewa daga APC.

Daga cikin waɗanda suka harci taron har da tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da tsohon ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu da Hon Farouk Adamu Aliyu, tsohon ɗan majalisar daga jihar Jigawa da wasu ƙusushin tsohuwar CPCn.

To sai toshon Ministan ya yi watsi da wannan iƙirari da tsagin Almakuran suka yi, yana mai bayyana matsayar tasu da ta raɗin kai ba da yawun tsohuwar tafiyar CPCn ba.

Cikin wata sanarwa da kakakin tsohon ministan, Muhammad Bello Doka ya fitar, ya ce jagorancin tsohuwar jam’iyyar CPCn ne kawai ke da alhakin fitar da matsayar tsohuwar jam’iyyar kan kan batun fita daga APC, ba tsagin su Almakura ba.

Malami ya zargi Tanko Al-Makura da Adamu Adamu da Aminu Bello Masari da kuma Farouk Adamu Aliyu ya janye jikinsu daga jikin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

Dangane da batun komawarsa jam’iyyar SDP kuwa, Malami ya ce aikin masu yaɗa jita-jita ne, amma ya ce yana kan tattaunawa da magoya bayansa kan batun.

“Malami fitaccen mutum ne a Najeriya, don haka ba zai fice daga jam’iyya a asirce ba, har yanzu yana APC, amma yana ci gaba da tattaunawa da magoya bayansa, idan ya kammala kuma zai bayyana matsayinsa”, in ji kakakin tsohon ministan.

legit com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp