Ƙwararre kan harkokin musayar ‘yan wasa, Fabrizio Romano, ya musanta jita-jitar yarjejeniya tsakanin Victor Osimhen da Liverpool.
A makon da ya gabata ne dai aka ruwaito cewa Liverpool ta kulla yarjejeniya da dan wasan na Najeriya.
Sai dai Romano ya bayyana cewa babu irin wannan yarjejeniya tsakanin manyan kungiyoyin Premier da Osimhen.
“Chelsea na sa ido kan Victor Osimhen. A Italiya wasu kafafen yada labarai na bayar da rahoton cewa Victor Osimhen ya riga ya amince da yarjejeniyar kwantiragi da Liverpool, “in ji shi a shafinsa na YouTube.
“Daga abin da aka gaya mini, a halin yanzu, Victor Osimhen bai amince da komai da kowace kungiya ba, har ma da Napoli, babu yarjejeniya kan tsawaita kwantiragin.
“Bai amince da komai da wata kungiya ba don haka Osimhen zai dauki lokacinsa. Rahotannin yarjejeniyar da aka riga aka yi da Liverpool ba gaskiya ba ne.
Makomar Osimhen ta sake tashi sama bayan taho mu gama da suka yi da zakarun Seria A.
Dan wasan mai shekaru 24 ya fusata ne da bidiyon TikTok guda biyu da kulob din ya buga suna yi masa ba’a bayan ya kasa bugun fanareti a karawar da suka yi da Bologna.
Ita ma Napoli ta fusata ne bayan da dan wasan ya dawo daga buga wasan kasa da kasa sakamakon raunin da ya samu a makon jiya.