Shugaban riko na jamâiyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum, ya yi gargadin cewa babu wanda zai iya tursasa shi ya yi murabus daga mukaminsa.
Damagum ya ce masu kiran ya yi murabus suna kara masa farin jini ne kawai.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitocin sasantawa da ladabtarwa na kasa, mukaddashin shugaban ya yi tir da masu yada labaran karya game da ayyukan kwamitin ayyuka na kasa.
“Bari in aika da sako ga duk wanda ke magana game da Damagum wannan, Damagum cewa – ba zan iya tsoratar da ni ba. Da zarar ka ambace ni, sai na samu farin jini,â in ji Damagum.
A farkon makon nan dai alamu sun nuna cewa kwamitin ayyuka na jamâiyyar PDP na kasa (NWC) na iya kakabawa Damagum da sakataren kasa, Samuel Anyanwu takunkumi kan wata wasika da ake zargin ya rubuta wa kotun daukaka kara da ke Fatakwal.
Ana dai kallon wasikar a matsayin wani abu na adawa da jamâiyyar, kuma wasu jiga-jigan jamâiyyar da suka hada da âyan kwamitin zartaswa na kasa (NEC) sun matsa kaimi wajen daukar mataki kan Damagum da Anyanwu.