Tsoshon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce mulkin demokradiyya ya gaza wajen kawo ci gaba a nahiyar Afrika.
Ya ce tsarin ya gaza ne saboda abin da ya ƙunsa bai zo daidai da al’adu, da yadda ake tafiyar da rayuwa a nahiyar ba, da abubuwan da mutanen nahiyar suka yi amanna da su ba.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abuja, babban birnin Najeriya, a wurin wani taron bikin cika shekaru 60 a duniya na tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilan ƙasar, Emeka Ihedioha.
Tsohon shugaban ya yi nuni da cewa idan aka kalli yadda tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln, ya bayyana tsarin dimokuradiyya da cewa gwamnati ce ta mutane da mutane ke jagoranta domin al’umma.
Inda ya ƙara da cewa tsari ne da ake domin kowa ya amfana, ba wai wani bangare na al’umma ba ko wasu mutane ƙalilan ba.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa kafin zuwan dimokuradiyyar ƙasashen yamma, Afrika na da nata tsarin shugabancin wanda ke kula da buƙatun kowa.
A cewarsa wannan tsarin shi ne dimokuradiyya, ba abin da ake kira dimokuradiyya ba a yau wanda ke bai wa shugabanni damar karɓar duk abin da suke so ba bisa ƙa’ida ba da kuma ta hanyar cin hanci da rashawa su ce wa mutane su je kotu idan suna da ja.