Wata ƴar ƙasar Amurka wadda ta amsa laifin jagorantar bataliyar mata a ƙungiyar IS a Gabas Ta Tsakiya za ta shafe shekara 20 a gidan yari.
Kamar yadda wata kotun Amurka ta yanke hukunci, Allison Fluke-Ekren ƴar asalin Jihar Kanzus ce ta Amurka kuma ta amsa laifinta.
Inda ta ce ta ba sama da mata ɗari manya da ƙanana horon soji inda ta ce wasu ma ba su wuce shekara goma ba.
Matar wadda ta musulunta an yi fasa kwabrinta zuwa Syria a shekarar 2012 inda ta zama cikakkiyar mamba a ƙungiyar ta IS da ke iƙirarin jihadi.
Bayan nan ta auri kwamandojin ƙungiyar da dama kuma ta rinƙa ba mata horo kan yadda ake amfani da bindiga ƙirar AK-47 da gurneti da kuma harin ƙunar-baƙin-wake