fidelitybank

Ba Amurke ya kashe ɗan shekara 6 saboda Musulman Falasɗinu ne

Date:

A na tuhumar wani mutum da laifin kisan kai da kuma nuna ƙiyayya bayan da aka zarge shi da caka wa wasu mutane biyu wuƙa saboda su musulmai ne a Amurka.

Ana zargin Joseph Czuba mai shekaru 71 da kashe wani yaro dan shekara shida da raunata wata mata mai shekaru 32 a Plainfield, Illinois da ke Amurka.

Ofishin babban jami’in ƴan sanda na yankin Will County ya ce, an kai musu hari ne saboda rikicin da ake yi a yanzu tsakanin Hamas da Isra’ila.

Shugaba Biden ya ce ya ji “bacin rai” kan harin da aka kai wa mahaifiyar da danta, waɗanda Falasdinawa ne mazauna ƙasar Amurka.

“Wannan mummunan aiki na ƙiyayya ba shi da gurbi a Amurka, kuma ya ci karo da aƙidunmu,” in ji Biden a cikin wata sanarwa.

“A matsayinmu na Amurkawa, dole ne mu hadu wuri guda, mu yi watsi da kyamar Musulunci da duk wani nau’i na son zuciya da kiyayya.”

A cikin sanarwar ta ranar Lahadi, ofishin ƴan sandan na Will County ya ce, a safiyar Asabar sun samu kiran gaggawa daga matar wadda ta ce wanda ya ba su hayar gida ne ya kai mata hari a yankin Plainfield, kusa da Chicago.

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp