Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya ce ƙasarsa na ”sanya idanu cikin tsanaki” game da labarin hatsarin jirgi mai saukar ungulu da ke ɗauke da shugaban Iran da ministan harkokin wajen ƙasar.
“A yanzu babu abin da za mu ce game da batun,”in ji shi.
Rahotonni daga ƙasar na cewa shugaba Biden ya samu labarin hatsarin jirgin na shugaban Iran.