Jam’iyyar PDP ta ce jam’iyyar APC mai mulki ba ta da wani abin nunawa ga ‘yan Najeriya.
Daraktan yakin neman zaben PDP na matasa a Jigawa, Malam Umar Danjani ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani ga kungiyar matasan APC.
Ya ce jam’iyyar PDP ce kadai a Najeriya da ta aiwatar da ayyukan raya kasa da ‘yan Najeriya ke alfahari da su.
A cewarsa “Gwamnatin APC ba ta da wani abu da za ta nunawa ‘yan Najeriya baya ga talauci da rashin tsaro da rashin shugabanci.”
Ya ce jam’iyyar APC tana cikin firgici kan karbuwar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da dan takarar gwamna a jihar Jigawa, Mustapha Sule Lamido.
“Muna jiran rantsuwa ne kawai domin babu shakka jam’iyyar APC za ta fadi kasa a zabe mai zuwa saboda babu abin da za su yi yakin neman zabe da shi,” in ji Danjani.